Shugabannin gargajiya na yankin Gembu dake jihar Taraba da ya yi fama da tashe-tashen hankula da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a sun yi kira a kai zuciya nesa don samun dawamammiyar zaman lafiya.
Sarkin Mambila Dokta Shehu Audu Baju na biyu ya furta haka lokacin da yake jawabi a fadarsa inda ya gargadi jama’a su ajiye makamai da daina yin kalamai masu sosa rai ko su fuskanci fushin hukuma tare da tabbacin gwamnati da jami’an tsaro a shirye suke don tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a.
Shugaban kungiyar Hausa-Fulani ta raya yankin Gembu Haruna Bakari Tanja ya yi kira da a zauna lafiya kana ya bukaci hukumomin tsaro su tsananta bincike wajen maidowa jama’a dukiyoyin da aka sace ko dauka a matsayin ganima.
Su ma wakilan al’umomi dake fada da juna na Mambila da Fulani Alhaji Umaru Zubairu da Alhaji Saidu Bawa sun yiwa jama’arsu gargadi cewa duk wanda ya dauki ganima sakamakon wannan tashin hankali ya maido da su, tare da bayana masifar da cewa kaddara ce daga Allah.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansanda ta jihar Taraba ASP David Misal ya ce bayaga harin sari-ka-noke da bangarorin ke kaiwa juna sun yi nasarar kwantar da tashin hankalin.
Wasu mazauna yankin kamar yadda Mohammed Hassan da Mohammed Bugare suka tabbatar wa Muryar Amurka hankula sun kwanta kuma jama’a na gudanar da al’amuran kasuwanci da hada-hadar tattalin arziki a yankin dake kan farfajiyar iyakar Najeriya da jumhuriyar Kamaru.
Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Your browser doesn’t support HTML5