A Syria Wani Hari Ya Hallaka Shugabannin Masu Tsatsauran Ra'ayi

Wani mayakin 'yan tawaye

A Syria, masu sa ido kan rikicin kasar suka ce wani hari da aka kai kusa da iyakar kasar da Turkiyya a daren Lahadi, ya halaka wasu shugabanni masu tsatsauran ra'ayi cikinsu harda wani kwamanda na reshen mayaka da galibinsu 'yan kalibar Uighurs daga yammacin kasar China suka fito.

Kungiyar ta rajin kare 'yancin Bil'Adama a kasar, wacce take sa ido sosai kan yakin basasar kasar, tace an kashe mutane takwas a harin da aka kai a arewacin lardin Idlib akan hanyar zuwa wurin da ake kira Sarmada dake kan iyaka.

Babu tabbas nan take wa ya kai harin , amma rahotannin daga kungiyar rajin kare 'yancin Bil'Adaman ya ce, bisa dukkan alamu rundunar taron dangi karkashin jagorancin Amurka waccce take fafatawa da masu tsattsauran ra'ayi a yankin ce ta kai harin.

Ahalinda ake ciki kuma, 'yan tawaye a Syrian suka ce zasu dakatar da shawarwari da suke yi na shiga shawarwarin sulhu da ake shirin za'a yi wani lokaci cikin watan nan a Kazakhstan, saboda abunda suka kira ci gaba da keta ka'idojin yarjejeniyar tsagaita wuta daga bangaren dakarun kasar.