A Spain 'Yan Awaren Catalona Sun Yi Arangama Da 'Yan Sanda

'Yan awaren Catalona da suke zanga zanga a gaban karamin ofishin jakadanci Jamus akan kama tsohon shugaban yankin Catalona, a kasarta Jamus

A Spain an yi taho mu gama tsakanin 'yan awaren Catalona dake zanga zanga da 'yan sanda dake neman hanasu

Masu zanga zanga, ‘yan awaren Catalonia, sun yi arangama da ,yan sanda a birnin Barcelonia, a Spain, yayin da suke macin nuna rashin amincewarsu da kama tsohon shugaban yankin Carles Puigdemont.


Yan sandan sun yi amfani da kulakai domin hana masu zanga zanga zuwa ga ofisoshin gwamnatin Spain. Masu macin sun jefi jami’an yan sandan da shara da wasu abubuwa. Akalla mutane 50 suka samu raunuka.

Dubban mutane ne suka mamaye titunan babban birnin Catalonia don nuna goyon shugaban yankin da aka tsige, mai ra'ayin 'yan aware, wanda aka kama bisa takardan sammacin kasa da kasa a kasar Jamus, a jiya Lahadi. Tsohon shugaban ya tsallaka kan iyaka daga kasar Denmark ya shiga Jamus.


Ana sa ran Puigdemont zai bayyana kotu a yau Litini a Schleswig, yayin da masu shigar da kara na Jamus suke nazarin bukatar Spain, na a mika mata shi.


Ana neman Puigdemont a Spain bisa zarginsa da laifin cin amanar kasa da kuma iza tashin hankali. Shugaban ya arce daga Spain zuwa Belgium ne a cikin watan Oktoba.