A Saliyo Dokar Hana Fita Na Kwanaki Uku Domin Yaki Da Ebola Ta Fara Aiki

Wani ma'aikacin kiwon lafiya yake kawo wata mace da ake tuhuma ta kamu d a cutar Ebola

A saliyo galibin titunan babban birnin kasar kusan babu kowa jiya jumma’a, a fara aiki da dokar hana fita na kwanaki uku a kasar domin gano masu fama da cutar Ebola da suka buya, a yunkurin dakile yaduwarta.

Dubun dubatan ma’aikatan kiwon lafiya a kasar da take yammacin Afirka suna bi- gida -gida domin wayar da kan jama’a kan hanyoyin kaucewa kamuwa da cutar da kuma kira ga wadanda suke da alamun cutar su je cibiyoyin kiwon lafiya.

Shugaban kasar Ernest Bai koroma yayi kira ga ‘yan kasar Saliyo su zauna gida daga jiya jumma’a da yau Asabar da kuma gobe lahadi, a jawabin da ya yiwa al’umar kasar ta talabijin yana cewa “irin wannan yanayi na ba kasafam ba, yana bukatar matakai na ba safam ba.”.

Cutar ta kashe fiyeda mutane dubu biyu da dari shida a fadin yammacin Afirka, mutane fiyeda 560 ne cutar Ebola ta halaka a Saliyo.

A makwabciyarta kasar Guinea kuma, mazauna karkara a can kudu maso gabashin kasar, sun kashe mutane takwas daga cikin wata tawagar masu aikin wayar da kai kan cutar ta Ebola.

Hukumomin kasar sun gayawa Sashen Faransa na MA cewa an kama mutane shida dangane da kisan, suna masu cewa wasu mutanen sun hakikance babu cutar Ebola, da zaton tawagar mutanen sun je ne domin su kashe su.