Da farkon wannan shekarar ne cedi wato kudin Ghana ya fadi warwas akan dala, yanayin da ya yi sanadiyyar tabarbarewar tattalin arzikin kasar, sannan a kullum ana samu hauhawar farashin kayayaki ga kuma tsadar rayuwa.
Sai dai bayan wata sanarwa a kwanan nan da asusun bada lamuni na IMF ya yi na cewa ya cimma yarjejeniya dala biliyan 3, da tsare-tsarensa na shekara uku, domin ceto kudin kasar (cedi) ya dinga farfadowa wanda tsakanin kwana 4 ya farfado da kaso 30% akan dala.
A bangare guda kuma duk da hakan farashin kayayyaki yaki sauka kasa lamarin da ya kai shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ga yin kira ga shugabanni kwadago da kungiyoyin ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki su da rage farashin kayayyaki.
“Ina dora muryata kan kira ga kamfanonin GUTA, GRTCC da sauran su, kuma na yi kira ga masana’antun, ‘yan kasuwa da masu sayar da kayayyaki, da sakamakon faduwar darajar cedi da aka samu a baya-bayan nan suka yi kare karen farashin kayyaki, da su rage farashin kayayyakinsu da na ayyuka, saboda cedi yana dawo da ƙarfinsa sosai.”
Wasu ‘yan kasuwan sun ce ba za su iya rage kayan ba saboda a lokacin da suka siyo kayan dala na sama akan cedi.
Sarki Imran Ashiru Dinken ya ce sai ya an kwashe watanni cedi na farfadowa akan dala kafin za'a iya cewa 'yan kasuwa su rege kudin kaya.
Saurari cikakken rahoton Hawa Abdul karim
Your browser doesn’t support HTML5