Kwana daya bayan sake bude makarantu a Jamhuriyar Nijer, dalibai a fadin kasar sun kauracewa ajujuwan karatu da nufin nunawa hukumomi bacin ran su game da rashin tanadin matakan kariya kanCOVID-19.
Kungiyar malaman kwantaragi ta ce, ta gano irin wannan matsala a makarantu da dama, sai dai gwamnati na cewa nan ba da jimawa ba za ta dauki mataki.
Kayayakin wanke hannuwa da takunkumin rufe fuska ne abubuwan da hukumomin ilimi suka yi alkwarin tanadarwa daukacin makarantu mallakar gwamnati domin kare dalibai daga kamuwa da annobar coronavirus, to sai dai a wunin farkon na sake bude makarantu bayanai na nunin ba a kai irin wadanan kayayakin ba a wurare da dama, yayin da a wasu makarantun dalibai ke zaune a filin Allah saboda rashin dakunan karatu, lamarin da ya sa kungiyar dalibai ta USN kiran magoya bayanta su kauracewa ajujuwa.
Sakataren kungiyar Ider Algabit ya bayyana wa wakilin muryar Amurka cewa, sun yi zagaye a makarantu da wurare da dama, amma sun gano akawai matsalar rashin matakan kariya akan kamuwa ko yaduwar cutar coronavirus.
Shuwagabanin kungiyar SYNACEB ta malaman kwantaragi sun ce, sun gano irin wannan matsala a wasu daga cikin makarantun da su ka ziyarta a ranar 1 ga watan Yuni. Sakataren kungiyar SYNACEB a yankin Yamai Soumaila Maiga Mahamadou ya ce, gaskia yaran su na cikin hadarin kamuwa da cutar, sobada ba matakan kariya da ake bukata.
Shugaban ma’aikata a ofishin Ministan ilimi a matakin Primary, Ashana Hima ya shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, gaskiya ne akwai wannan matsala, amma gwamnati ta na iya kokarinta na ganin abubuwa sun daidaitu nan dan lokacin kadan.
A ranar 20 ga watan Maris hukumomin Nijer suka ba da sanarwar rufe makarantu a fadin kasar, bayan gano mutun na farko da ya kamu da cutar coronavirus.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5