Tace yanzu yanayi ya canza saboda haka dole ne wanda yake son ya rayu ya kirkiro sabon abun.
Idan aka yiwa wasu sana'o'in gargajiya kwaskwarima ko shakka babu za'a samu cigaba kana kowa ya ci anfaninsu..
Kungiyar ta Yauwa tace tana da tallafin da take kawowa mata har ma da matasa maza inda suke bada kudi wanda mace taza dinga juyawa kan aiki sabo da wanda ya karbi kudin zai kirkiro.
Hajiya Malle Malam Aji jagorar kungiyar mata ta Mun Tashi tace sun karu da horon da suka samu. Sun koyi sabbin dabarun shugabanci da zasu taimakesu yiwa matansu jagoranci na gari.
Ita ma Hajiya Maryamu Mamman ta kungiyar Dimar tace babban mahimmancin abu shi ne mata su hada kansu. Hadin kai zai hana wadanda suke son su kawo matsala tsakaninsu cin nasara.
Kungiyoyin dai sun nuna cewa horon yayi masu dadi. Sun karu dashi sun kuma ci anfaninshi.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5