Jita jitar da ake yayatawa na cewa jam'iyyar ta MNRD tana shirin yiwa jam'iyyar MNSD zago kasa saboda shigarta gwamnatin PNSD ya sa ta fitar da wata sanarwa.
Sun musanta batun cewa suna shirin canza sheka zuwa PNDS saboda dangantaka dake tsakanin shugaban kasa da shugaban jam'iyyar ta MNRD, abun da ta kira shati fadi.
Alhaji Sedu Yakuba mataimakin shugaban jam'iyyar MNRD Hakuri yace 'yan Nijar na ciki da na ketare su sani babu wani shirin canza sheka. Yace MNRD Hakuri tana nan gungunta na adawa.
Yace idan ana tafiyar siyasa a kasa ya kamata a ce akwai adawa. Idan an yi la'akari a lokacin da suka gabatar da Mahamman Usman a matsayin dan takara kokari aka yi a takure ko a tauye dimokradiya a kasar
Inji Mahamman Usman tsayar da dankarar da suka yi ya ba dimokradiya dagalaba. Haka ma a wannan tafiya da ake yi sun lura cewa wannan gwamnati ta Mahammadou Issoufou so tak yi ta mayar da adawa gefe guda. Yace su jam'iyyarsu ta matasa bata yadda da kawar da adawa ba.
To saidai jam'iyyar PNDS Tarayya ta musanta yunkurin durkusar da dimokradiya a karkashin shirin gwamnatin hadaka kamar yadda kakakinta Asumana Muhammadou ya fada. Yace duk wadanda suka san ciwon kasa sun amshi gayyatar shugaban kasa kamam irinsu MNSD.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5