Kusan kowane irin kayan masarufi kama daga madarar gwangwani zuwa taliya suna cikin kayan da aka kone.
Hukumar Cinikayya ta yankin Damagaran ta kwace kayan a wasu shaguna dake birnin garin.
Daraktan hukumar Namata Insha yace zasu cigaba da aikin har sai sun tabbatar ana sayarwa jama'a kayan masarufi nagatattu domin kiyaye lafiyar jama'a. Sun bukaci jama'a su basu goyon baya akan aikin da su keyi a kuma duk lokacin da suka fita yin aikin.
Yace sun yi aikin ne da goyon bayan wasu hukumomin gwamnati irin su 'yansanda da kwastan da masu kula da shige da fice.
Malam Isa Musa da ya jagoranci bikin kone kayan ya kira 'yan kasuwa su dinga kula da kayan da suke sayarwa al'umma domin a kiyaye kamuwa da cututtuka.
Yace hukumar cinikayya nada ikon shiga shaguna su duba kayan dake ciki idan kuma sun ga wanda wa'adinsa ya kare wajibi ne su kwace su kuma kone.
Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5