Wasu matsaloli da suka dade ana fama dasu suka sa kungiyar daliban Nijar ta kira daliban kasar su kauracewa komawa karatu bayan da babban hutunsu ya kare jiya.
Malam Tsalha Kaila mataimakin magatakarda na kungiyar daliban jami'ar Yamai yana mai cewa kudaden da ya kamata a ba dalibai a watan Afirilu har zuwa wannan lokacin ba'a ba su ba. Akwai kuma kudaden da yakamata a biya yanzu amma tun da ba'a biya na baya ba "ba'a tunanen biyan na yanzu" inji Kaila
A cewarsa shugabannin jami'a sun ki su inganta harkokin karatau. Ta bakinsa akwai daliban da sai sun labe a wajen taga su daukai karatu. Wasu ma sai sun je karkashin bishiya kafin su samu daukan karatu. Dalili ke nan da daliban suka ki komawa karatu.
Sai dai gwamnatin Nijar ta dora laifin kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar wanda ya kawo jinkiri wajen warware matsalolin.
Su kuma shugabannin daliban na cewa abu daya zai sa su amince da ikirarin rashin kudi da gwamanatin ke yi. Idan yau shugaban kasa da firayim ministan kasar sun daina daukan albashi ko sun koma karban rabi, daliban zasu yadda da cewa lallai akwai tabarbarewa tattalin arziki. Inji daliban, yin hakan zai samar da kudi wa wasu wuraren.
Ministan Ilimi Mai Zurfi Yahuza Sadisu ya shaidawa Muryar Amurka cewa yana da kwarin gwuiwa zai samu yin sulhu da daliban nan ba da jimawa ba.
Ga rahoton Souley Barma ba karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5