Rashin samun amsa mai gamsarwa daga bangaren hukumomi akan bukatar maido da tsarin zaben shuwagabanin jami’o'i a maimakon tsarin nadi da gwamnatin ta Niger ta kudiri aniyar shimfidawa ya sa kungiyar SNECS ta umurci magoya bayanta su jingine aiki daga yau Litinin.
Na Bala Adare shine sakataren kungiyar malaman jami’oin ya ce gwamnati ce ta take doka saboda dokar ce ta ce dole ne a zabi shugaban jami'a ba a nadashi ba kamar yadda gwamnati ke neman yi yanzu.
A taron manema labaran da ya kira don bayyana matsayin gwamanati akan wannan dambarwa, ministan ilimi mai zurfi YAHOUZA SADISSOU ya bayyana cewa hukumomi na nan akan bakarsu. A cewarsa a duka kasashen Afirka babu inda ake zaben shugaban jami'a sai Niger. Koina gwamnati ce take dubawa ta ga wanda ya dace a ba mukamin. A cewarsa dalili ke nan da gwamnati ta ce nan gaba ita ce za ta dinga nada shugaban jami'a. Wannan hanya ce kadai da za ta basu damar shawo kan wasu matsaloli, injishi.
Batun wasu kudaden alawus da aka jima ba'a biya malaman jami’oin ba da matakin zaftare albashi da gwamnatin ta dauka akan malaman da suka tsunduma cikin yajin aiki na daga cikin abubuwan da kungiyar SNECS ta ce ba za ta lamunta da su ba. Na Bala Adare ya ce kokensu akan a biyasu kudinsu dole sai an koma kan dokar kudi domin a yi maganin abun.
Minista YAHOUZA SADISSOU wanda ya yi wa malamai tayin sulhu ya shawarci wadanda ba su aminta da zaftare kudaden albashinsu ba su kai maganar gaban kotu. Ya ce koke koken da suka kawo ba dalili ba ne na shiga yajin aiki na kawana da kwanaki. Saboda haka bisa doka ya rubuta wasika a yanke masu albashi gwargwadon kwanakin da ba su yi aiki ba. A cewarsa doka ce ta bashi damar yin hakan. Idan kuma akwai wanda bai yadda da matakin ba sai ya garzaya kotu ya shigar da kara. Idan kotu ta basu gaskiya za'a biyasu.
A saurari rahoton Souley Barma.
Your browser doesn’t support HTML5