A Netherland Yanzu Hukumomin Tsaro Na Iya Leken Sakonnin Internet

Taron 'yan jarida da Shugaban kasar Netherland

Masu jefa kuri'a a Holland, jiya Laraba, sun amince da wani kuduri da aka yi kuri'ar raba gardama akansa na baiwa hukumomin leken ikon kallon sakonnin internet, a kuma dai dai lokacinda labarai suka fito cewa kamfanin Facebook da ya kyale aka yi amfani da bayanan mutane miliyan 50, wanda ya sake maido da muhawara kan batun sirrin bayanan mutane a dandali ko shafukan sada zumunta.

A wannan kuriar ta jin ra'ayin jamaa bayan sun kada kuri'a ya nuna cewa kashi 49 sun amince da samar da wannan sabon tsarin yayin da kashi 48 suko suka ce basu amince ba, sai dai wannan kuria'ar ba tilas ba ce sai an yi aiki da ita.

Kudurin ya bukaci amincewar 'yan kasar ne akan barin jami'an tsaro su dinga leken sakonnin da ake aikawa ta internet

Yanzu dai Prime ministan kasar zai bar doka tayi aikin ta, dominko batu ne da majilisun dokokin kasar duka suka amince dashi.

Prime Minisitan yace ba wai munyi haka bane domin kasar mu tana cikin wani hatsari ko barazana ba, a’a wannan matakin zai kara wa kasar tsaro.

Ahalinda ake ciki kuma shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg, a hira d a yayi da kafofin yada labarai daban daban a jiya Laraba, yace a fili yake kamfaninsa ya yi kuskure a irin rawar da ya taka a tara bayanan mutane ba bisa ka'ida ba.

"Wannan babbar cin amana ne. Ina matukar nadamar faruwar haka. Muna da hakkin ganin kare bayanan mutane," Zuckerberg ya gayawa tashar talabijin ta CNN.