Mutane 2673 ne suka rasa rayukansu sakamakon sakamakon haduran mota a Najeriya daga watan Janairu zuwa na Yunin bana.
Hukumar kidigdiga ta Najeriya ce ta wallafa bayanin a sashenta. Ta gano cewa gudun tsiya shi ne babban dalilin dake kawo hatsari. Akwai kuma yankewar birki da tukin ganganci da yawancin direbobi ke yi.
A Abuja aka fi samun munanan hatsura inda ko a cikin gari wasu kan runtuma kan mil dari da talatin. A kan titi daya tana yiwuwa wani ya karawa wani ko kuma ya shiga cikin karkashin wata motar saboda yana cikin maye.
Babban jami'in direbobin Najeriya Suleman Zaki yace duk inda aka ce direba yana awa biyar yana tuki wajibi ne a tilasata masa ya huta amma ba a cikin mota ba. Dole ne ya samu wurinda zai kwanta ya mike.
Hukumar hada-hadar kasuwanci ta jiragen ruwa ta sanar da shirin kafa tasoshin shakatawar direbobi domin dauke manyan motoci daga hanya.
Hassan Bello shugaban hukumar yace da zara an kammala tasoshin babu wani wuri kuma da za'a ajiye manyan motoci.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5