A Najeriya Ana Tafka Muhawara A Majalisance Kan Cin Bashin China

Buhari da Xi

Bayan Najeriya ta ciwo bashin Naira triliyan daya da digo biyar cikin watanni shida kacal, ta sake kai kokon bara zuwa Kasar China, inda ta ke neman bashin dalar Amurka biliyan 5 da digo 3 domin tallafo aikin layin dogo daga Ibadan zuwa Kano. Wannan na cikin bayanan da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya yi a lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Sa Ido kan yarjjeniyoyi da kuma Basussuka Na Majalisar Wakilai.

An yi musayar yawu da tada jijiyar wuya a lokacin da Shugaban Kwamitin da ke sa ido akan sha'anin yarjejeniya da kuma basusuka na Majalisar Wakilai, Osai Nicholas Osai yake yi wa Ministan Sufuri Rotimi Amaechi tambayoyi akan yadda ake karbar basusuka da kuma yadda za a biya.

Bayanan da Ministan Sufurin ya bayar ba su gamsar da Kwmitin ba domin sun ce sun gano cewa Ma'aikatar Sufurin ta sanya hannu kan kwangilar kasuwanci wacce darajarta ta kai dala biliyan 33 ba tare da wani ingantaccen tsarin hanyoyin biyan basusukan ba. Amma Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ce kwangilar da Gwamnatin Buhari ta riga ta sa hannu akai, itace ta dala biliyan daya da digo 6 kuma an yi amfani da kudin a aikin layin dogo dag Legas zuwa Ibadan, sannan akwai ta dalar Amurka miliyan 800 da Gwamnatin Goodluck ta sa hannu kafin ta sauka.

Wani abu da ya kunno kai shi ne tunanin mika wuya game da diyaucin Najeriya da wannan al'amari yake neman ya janyo, amma Kwararre a fanin Kundin tsarin Mulkin Kasa da shari'a, Barista Mainasara Ibrahim Umar ya ce tun 1812 ne aka fara irin wannan yarjejeniyar daga kasar Amurka, kuma duk kasar da ta bada bashi sai ta nemi wani abu da zai zama mata lamuni domin kar a zo ba a biya bashin ba, saboda haka a shari'ance an amince da haka.

To sai dai kwararre a harkan tattalin arzikin kasa, Shuaibu Idris Mikati ya ce cin bashi ga kasa mai tasowa irin Najeriya ba laifi ba ne idan an yi la'akari da yadda cutar Coronavirus ta yi kacakaca da tattalin arzikin kasashen duniya. Mikati ya ce hikima za a bi wajen biyan basusukan saboda kar ya shafi kamfanoni da yawa domin suna iya durkushewa.

Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya Da Bashin China