Wani malami daga Damaturu ya yi murnar dawo da 'yan matan, amma ya zargi gwamnatin tarayya cewa tana da hanu a sace su da kuma dawo dasu.
Akan rashin dawo da daya daga cikin 'yan matan wai domin ta ki shiga muslunci ya sa Shaikh Bala Lau cewa hakan ba musulunci ba ne domin babu batun dole a shiga addinin.A cewarsa abun da suka yi ba addinin musulunci ba ne.
A can jihar Neja gwamnatin jihar ce ta jinjinawa gwamnati Shugaba Buhari. Gwamnan jihar yayi kira da a tashi tsaye a kare 'yan mata cikin makarantun su. Shiko Abdulkadie Na Funtuwa, ya alakanta sako 'yan matan ne da jajircewar Shugaban Kasa Muhammad Buhari akan lamarin. Shugaban wani kamfanin jarida ya ce nan gaba suna da tambayoyi da zasu yi.
Ita ko gwamnatin Najeriya cewa ta yi an sako 'yan matan ne tare da taimakon wasu kasashe kuma wai an yi hakan ne ba tare da wasu sharadi ba.
Aisha Yusuf, jigo a kungiyar BBOG dake fafutikar ganin an sako 'yan matan, ta ce suna farin ciki tare da kiran gwamnati ta fito ta yiwa jama'a bayani idan aka yi la'akari da yadda abun ya faru da kuma yadda aka dawo dasu.
Kafin a sako 'yan matan sai da jami'an tsaro suka dakatar da ayyukansu na wani dan lokaci wanda ya hada da dokar hana fita a garin Dapchi. Wannan mataki yasa Kwamred Isa Tijjani ya yi tsokaci. Ya ce Shugaba Buhari aka auna. Wani kuma cewa ya yi kasuwa ce ta bude wa wasu a Najeriya. A cewarsa yakamata shugaba Buhari ya sa ayar tambaya akan duk jami'an sojoji da na tsaro. Shi ma Dr Umar Ardo, daya cikin shugabannin PDP, ya ce akwai lauje cikin nadi a wannan lamarin. Yadda aka sace 'yan matan baya yiwuwa sai da hannun gwamnatin tarayya.
A saurari cikakken bayanai a wadannan rahotanni uku
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5