A Masallatan Juma’a Za a Yi Idin Bana - Sarkin Musulmi

Mai Martaba Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar na uku ya ce bana za a gudanar da Sallar Idin ne a masallatan Juma’a.

Hakan dai sabanin yadda al’ummar Musulmi suka saba taruwa ne a duk shekara don gudanar da sallar ta idi bayan kammala azumin watan Ramadan.

Mai Martaba ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da wasu shugabannin al’umma da ke cikin jihar Sokoto su 86, dangane da abin da ya shafi sallar idi da kuma wasu batutuwa daban.

Ya kuma bukaci shugabannin da su gargadi jama’arsu akan yin biyayya da wannan matsaya da aka cimma a jihar Sokoto da ma wasu jihohin kasar.

Mai Martaban ya kuma yi kashedi ga jama’a akan cewa kada su yi tunanin ana yunkurin hana su sallar Idi ne, amma an dauki matakin ne domin kare lafiyar al’umma sakamakon annobar cutar COVID-19.

Ya kuma ja hankalin iyayen kasa akan su ci gaba da kokarin da suke yi wajen ganin cewa an dakile cutar ta COVID-19.

Mazauna jihar sun bayyana mabambantan ra’ayoyi game da wannan mataki inda yayin da wasu ke maraba da matsaya wasu kura nuna akasın hakan suka yi.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Muhammadu Nasir.

Your browser doesn’t support HTML5

A Masallatan Juma’a Za a Yi Idin Bana - Sarkin Musulmi