A majalisar dokokin Amurka an cafke mutane dari uku masu zanga-zanga

Masu zanga zanga a harabar ginin majalisar dokokin Amurka da 'yansanda suka tsare

Akalla masu zanga-zanga guda 300 aka cafke a jiya Litinin sakamakon tattaki zuwa Majalisar dokokin Amurka da ke nan Washington suna dauke da jerin bukatunsu bayan sun ki yarda su bi umarnin barin wajen, kamar yadda ‘yan Sandan na Majalisar suka bayyana.

Mutanen da suka kira kansu da sunan masu rajin tsarkake Dimukuradiyya wajen wayar da kan al’umma game da yadda cibiyar kasuwanci ta Wall Street ke bindiga da kudade wajen cicciba ‘yan takarar siyasa.

Zanga-zangar da ta yi kama da wadda aka taba yi ta mamaye Wall Street don dakile yin Siyasar kudi. Abinda masu zanga-zangar suka ce siyasa ya kamata ta zama kofa ce a bude ga kowa ba tsirarun da ke neman alfarma a kasuwancinsu ba.

Wadannan mutane sun bayyana cewa ya kamata su fito ne don wayar da kan jama’a game da wannan hange nasu da suke ganin zai iya yiwa siyasa nakasu. Sun bayyana cewa suna bukatar yin haka don nuna wannan abu a matsayin rashin da’a ga jama’a.

Masu zanga-zangar sun rike kwalaye da ke dauke manyan kalaman suka game da siyasar kudi, sannan suka dinga daddaga kwalayen a daidai tagogin majalisar tare daga murya da a Turance dake cewa, “KU YI AIKIN KU – KUYI AIKIKU”.