Ma'aikatan kwadagon Najeriya musamman a jihar Legas sun yi watsi da kiran da United Labor Congress ko ULC ta yi na cewa su fara yajin aikin gama gari na har "sai baba ta gani".
Alamu sun nuna cewa ma'aikata da dama sun fita zuwa wuraren ayyukansu musamman a bankuna da gidajen mai da filayen jiragen sama. Bankuna sun kasance a bude kuma kwastamominsu na shiga da fita. Yawancin ma'aikatan sun ce basu da labarin wani yajin aiki.
Kodayake ministan kwadago Dr. Ngige ya ce kungiyar ta ULC haramtaciya ce saboda bata da rajista amma shugabanta Mr. Ajero ya ce bata bukatar amincewar ministan domin samun halarci a kasar. Ya cigaba da cewa ko kungiyar TUC sai da ta gudanar da ayyukanta na tsawon shekaru 27 kafin ta samu rajista amma hakan bai hanata gudanar da ayyukanta ba.
'Yan Najeriya na ganin cewa kiran yajin aikin na son kai ne kawai saboda haka ba zai yi wani tasiri ba.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5