Mummunan tarihi ya sake maimaita kansa a birnin Accra na kasar Ghana, inda irin mummunar fashewar nan da ta auku bara, ta sake aukuwa kuma an samu mace-mace.
WASHINGTON D.C. —
Wata fashewa mai girma, wadda ta auku a wata tashar mai, ta kada Accra, babban birnin kasar Ghana jiya Asabar, inda ta haddasa wata wuta mai girman gaske, wadda ta tilasata ma mazauna kusa da wurin gudu.
Ba a yi bayani game da wadanda abin ya rutsa da su ba, kodayake kafar labarai ta Reuters ta ruwaito Mataimakin Ministan Yada labarai Kojo Oppong Nkrumah na cewa, wasu mutane sun mutu, sannan wasu da dan dama sun samu raunuka. Bai bayyana adadin wadanda su ka mutu din ba.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Ghana Billy Anaglate, ya gaya ma kafar labaran Faransa AFP cewa, wata motar tanka ce ke juye mai a wani gidan mai sai fashewar ta auku.