: 'Yansanda a kasar Austria sun tilasta ma mata Musulmi kwaye fuskokinsu, bayan da dokar da ta haramta rufe fuska ta fara aiki.
Tun daga jiya Lahadi, sanya duk wani abin rufe fuska sosai harda irin wanda 'yan gudun fanfalaki na farar kankara ke sakawa , da wanda ake rufe fuska da shi lokacin tiyata idan ba a asibiti ba da kuma wanda ake sawa a wajen wassanin holewa, duk sun hanu cikin jama'a.
Duk wanda ya saba ma dokar kuma za a ci shi tarar dala 180. An kuma baiwa'yansanda damar su yi amfani da karfi muddun mutum ya ki kwaye fuskarsa.
Gwamnatin ta Austria ta ce dokar, wadda ta wajabta bayyana fuska tun daga karshen gashin goshi zuwa kumatu, an kafa ta ne don kare yanayin rayuwar 'yan Austria.
Sai dai Kungiyoyin Musulmi sun yi Allah wadai da wannan dokar, su na masu cewa wasu 'yan tsiraru ne kawai daga cikin al'ummar Musulmin Austria kan lullube dukkan fuskokinsu.
Dokar, wadda ta yi kama da wadda aka taba kafawa a kasashen Faransa da Belgium, ta na aiki har kan 'yan yawon bude ido ciki har da dinbin Larabawan da kan je hutu a wannan kasar mai tsaunuka.