Donald Trump ya fadawa manema labarai a jiya Alhamis cewa “Muna fatan maida wannan al’amarin bayanmu.”
Rikice rikicen sun hada da Korar tsohon Daraktan hukumar binciken Manyan Laifuka FBI James Comey yayin da ake zargin Trump ya bukaci Comey ya dakatar da binciken tsohon mai bashi shawara kan harkokin tsaro Micheal Flynn. Haka kuma shugaban na fuskantar tambayoyi dangane da alakar sa da Rasha a yayin takarar shugabancin kasa da kuma zargin bayyana bayanan sirri na tsaro ga Ministan Harkokin wajen rasha a yayin tattaunawar su a ofishin shugaban da ake kira Oval Office.
Wuraren da zai yada zango a yayin wannan tafiyar sun hada da Saudi Arabia, Israila da kuma Vatican, Wurare uku masu alfarma na addinai.
A ziyarar sa ta Saudi Arabia, Trump wanda ya kasance mai suka da kuma rashin yarda da Musulmai da har yayi kokarin hana Musulmai shiga Amurka, zai yi Magana akan addinin Musulunci a gaban shuwagabannin Musulmai, Mai baiwa Trump shawara kan harkokin tsaro H.R. McMaster yace shugaban kasa na fatan ganin zaman lafiya a addinin Musulunci.