A karon farko, wani mutum dake dauke da kwayar cutar kanjamau mai karya garkuwan jikin Bil Adama ta HIV ya bada gudunmuwar kodarsa gawani mutum wanda shima yana dauke da irin wannan cutar.
A Ranar 25 ga watan Maris ne, wani jerin kwarrarun likitotcin asibitin Jami’ar Johns Hopkins dake garin Baltimore na Amurka suka samu nasarar yin dashen kodar daga mai dauke da cutar HIV zuwa ga daya mutumen da shima yana fama da irin wannan cutar.
“Ita dai wannan cuta mai karyar garkuwar jiki da ta dade tana hallaka mutane tun a shekarun alif dari tara da tamanin, amma a yanzu an shawo kan cutar inda har masu dauke da ita zasu iya ceto rayuwar wasu ta hanyar bada gudumuwar kodarsu ga masu cutar”, a cewar Dr Dorry Segev, wani farfesa akan fida na Jam’ar Johns Hopkins a lokacinda yake yi wa manema labarai bayanin a ranar Alhamis
A inda aka fiton nan, an taba musayar wasu fannonin jiki a tsakanin mutanen dake dauke da kwsayar cutar HIV, amma da yake Kwayar cutar HIV na haddasa ciwon kwoda, mafi yawancin masu dauke da kwayar cutar basu iya bayar da gudunmuwar Kwodarsu.
DR Segev, yace shi da Abokanan aikinsa sunyi bincike akan sama da mutane 40,000 masu dauke da kwayar cutar HIV, inda suka gano cewa mutanen da ke dauke da kwayar cutar kuma suna shan magani kwodarsu na dai-dai da mutanen da basu dauke da cutar, kuma zasu iya bayar da kwodarsu ga mabukata.
Sannan kuma an gano cewa yanzu akwai magungunna da dama dake taimakawa mutanen dake dauke da kwayar cutar HIV su dade suna morewa rayuwarsu.