Tarihi ya mai-maita kan shi, shahararren dan wasan kwallon kafa dan kasar Algeria, mazauni kasar Ingila Riyad Mahrez. Ya zama mutun na farko a kasashen Afrika, da ya fara samun lambar yabo a wasan zakaru na kungiyar kwallon kafar kasashen Turai na shekarar 2016.“Premier League, PFA”
Dan wasan dai yana buga ma kungiyar kwallon kafar “Leicester City” ne, kana dan wasan Riyad, dai ya na matukar jin dadin wannan kakar wasan, inda ya samu damar saka kwallaye goma sha bakwai 17, kana ya taimaka wajen saka kwallaye goma sha daya 11, duk a cikin wannan kakar wasanin.
Riyard, mai buga wasan kasa-da-kasa ya yi rawar gani a lokacin gasar, hakan yasa aka karrama shi da wannan lambar yabon a dakin taro na Otel din Grosvenor a babban birnin Ingila. An bayyana dai yanzu haka suna neman karin maki biyar ne kawai su zamo zakaru a gasar wasan, wanda hakan zai zama abun tarihi na farko a duniya idan suka lashe wasan.