Wannan tattaunawa dai na zuwa ne alokacin da tashin hankali ya haifarwa da mutane barin gidajensu daga bangaren masu amfani da harshen ingilishi zuwa bangaren masu amfani da harshen Faransanci inda mutane ke matukar bukatar taimako.
Firai ministan Kamaru Joseph Dion Nguta, lokacin da ya kai ziyara garin masu amfani da Ingilishi Bamenda ranar Asabar, ya roki mutane da su shawarci ‘yan uwansu da suka shiga kungiyar mayakan ‘yan aware su koma gida.
Dion Nguta ya ce shugaban kasa Paul Biya ne ya aika shi ya fada musu ya shirya bin duk wata hanyar sasantawa, amma banda maganar raba ‘kasar Kamaru.
Ya yin da Firai Ministan yake yawon rokon zaman lafiya, rundunar sojojin Kamaru sun bayyana cewa yaki da ‘yan awaren na ‘kara tsanani, inda aka ruguje musu sansanoninsu tare da kashe mayaka sama da 20.
Flora Yenos mai shekaru 38 dake mafaka a Majami’ar Katolika ta Obili a babban birnin kasar Yaounde ta ce ta gujewa fadan da ake yi ne makon da ya gabata, daga kauyenta Bafanji dake yankin masu amfani da ingilishi a yankin Arewa maso Yamma. Tace ta rasa mijinta a lokacin wani fada da sojoji.
Ta ce lokacin da ta isa birnin Yaounde, ita da ‘ya ‘yan ta hudu basu da wani abin da zasu ci ko su sha, balle ma wajen kwana. Ta ce Majami’ar Katolika ce ta basu damar kwanciyar a azuzuwa, suka kuma nemi kristoci da su taimaka musu, duk kuwa da cewa tun farko ‘yan uwanta sun fada mata cewa ba zasu iya taimaka mata ba, saboda yanzu haka suna da wasu ‘yan gudun hijirar da suke taimakawa. Tace yaranta suna fama da rashin lafiya da yunwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 500,000 aka raba da gidajensu saboda fadan da ake yi.
Allegra Baiocchi, mai shirya tsare-tsare ma Majalisar Dinkin Duniya a Kamaru, ya ce a kullum mutane na ci gaba da neman tallafi.
Ya ce “muna sane da yawan mutanen dake cikin bukatu a bangarori daban-daban kamar bangaren lafiya da Ilimi da neman kariya, ahaka kuma ina tunanin ana ta kokarin taimakawa mutane.
A makon da ya gabata, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce mutane 1,800 aka kashe a yakin, haka kuma tace tana da shaidun dake nuna gwamnati tana kama ‘yan aware tana gallaza musu, yanzu haka ta na rike da wasu.
Illiaria Allegrozzi babbar mai bincike a kungiyar Human Rights Watch a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce “Mun sami bayanai daga wasu da aka taba rufewa a baya da ‘yan uwansu da kuma lauyoyinsu, haka kuma mun sami bayanai daga wasu kwararru dake duban hotuna da hotunan bidiyo na irin gallazawa da cin zarafin da ake yiwa wadanda aka Kaman.
Kungiyar Human Rights Watch ta ce tana kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya yi Allah wa dai da gallazawar da ake yiwa mutane, da kuma kira ga gwamnati ta kawo karshen wadannan abubuwan da suka fara faruwa tun lokacin da rikicin ya fara.
Ministan harkokin cikin gida na Kamaru, Paul Atanga Nji ya ce alhakin kame-kamen mutanen da ake da kashe-kashe da gallazawa ya rataya ne kan ‘yan aware. Ya ce a yunkurin gwamnati na samar da zaman lafiya za ta iya yafewa mayakan da suka ajiye makamansu.
Domin karin bayani saurari rahotan cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5