A Karon Farko Cikin Shekaru 50 Jiragen Amurka Zasu Fara Sauka Kasar Cuba

Kasar Cuba na kan shirye-shirye don saukar da jirgin saman Amurka na matafiya zai yi, a karon farko a wannan kasar ta Kwaminest cikin sama da shekaru 50, wanda shi ne na baya bayan nan a kokarin maido na hulda tsakanin kasashen biyu.

Shugaban Cibiyar Harkar Jiragen Sama Na Farar Hula, Alfredo Cordero ya ce kasar Cuba za ta kasance a shirye don zuwan da jirgin zai yi wannan satin da kuma zirga-zirgar dinbin jiragen Amurka wanda ake ganin ka iya yawaita har zuwa 110 a rana guda cikin shekara da dama masu zuwa.

Mataimakin Ministan sufurin Cuba Eduardo Rodriguez ya tabbatar da wannan hasashen, ya kara da cewa, "Filin jirgin saman Cuba ya jima ya na shirye-shirye cikin shekarun da su ka gabata saboda karuwar 'yan yawon bude ido."

Gobe Laraba ne dai jirgin fasinjan Amurka zai yi sauka ta farko, bayan da jirgin na Jet Blue zai tashi daga Fort Lauderdale na Florida zuwa birnin yankin tsakiyar Cuba na Santa Clara.

Sauran kamfanonin jiragen saman Amurka da ke shirin zirga-zirga zuwa Cuba sun hada da American Airlines, Frontier Airlines, Silver Airways, Southwest Airlines da kuma Sun County Airlines.

Har yanzu dokar Amurka ta haramta wasu harkoki na yawon bude ido a Cuba. To amma, Shugaba Barack Obama ya halatta wasu nau'uka na tafiye-tafiye, ciki har da ziyarar iyalai, da harkokin diflomasiyya, da na 'yan jarida da na batun ilimi.