An kwashi sa'a daya da rabi ana musayar kalamai da tada jijiyar wuya, tsakanin lauyoyi masu kare mai shari'a Walter Ononge, a karkashin jagorancin Wole Olanipekun da lauyoyin bangaren gwamnati wanda mai shari'a Aliyu Umar ya jagoranta.
Alkalin Alkalai bai isa kotun ba, amma daga karshe an daga shari'ar zuwa ranar Talata 22 ga watan Janairun wannan shekarar.
Ganin cewa wannan shine karo na biyu da za a gurfanar da wani babban mai mukami a wannan gwamnatin a kotu, a bisa tuhumarsa da laifin kin bayyana kaddarorinsa da kuma dukiyar da ya mallaka.
Laifin da ka iya kai shi ga dauri a gidan kaso na lokaci mai tsawo, gwararre a fannin siyasa kuma malami a Jami'ar Abuja Dr. Abubakar Umar Kari, yayi sharhi akan hakan inda yake cewa, yana ganin gurfanar da wannan dan talikin babban al'amari ne, abu ne mai tayar da kura, da zai sa da'awar da gwamnatin Buhari ke yi na cin hanci da rashawa akan faifai.
Amma daya daga cikin lauyoyi 42 da suka bayyana a kotun, don kare Walter Onongen mai suna Oritsaje Nbonwun, ya ce hukumar kula da harkokin Shari'a ta kasa ce ya kamata ta fara tuhumar Alkalin Alkalan, da duk wani laifi da ake tuhumarsa da shi kafin a gurfanar da shi a gaban kotu, kuma ba wannan kotun ne ya kamata a kawo shi ba, wannan kotun ba ta da hurumin sauraron shari'ar, hakan bata lokaci ne kawai suke yi.
Bayan an daga shari'ar ne wasu lauyoyi suka dauki kwalaye suna zanga-zangar nuna goyon bayansu ga wanda ake tuhuma.
Ga rahoton Medina Dauda daga birnin tarayya Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5