Dangane da dambarwar dake gudana a Najeriya da ta hada da batun matasan arewa dake cewa 'yan kabilar Igo su tattara nasu i nasu su bar jihohin arewa nan da watanni uku, ya jawo martani daga sassan Najeriya daban daban.
'Yan kabilar Igbo dake zaune a yankinsu da 'yan arewa dake zaune cikinsu sun mayar da martani bisa kalamun 'yan arewa.
Yan kabilar Igbo sun tofa albarkacin bakunansu. Cyril Okeke cewa yayi abun dake faruwa ya isa. Kamata yayi al'ummar Igbo su daina ambatar Biafra koina ko kuma kyaushe domin samun zaman lafiya.Yace ya isa haka. Yace gaskiya ba sa son 'yan arewa su bar yakinsu.Haka ma baya son 'yan kabilarsu su bar arewa.
Amma wani kuma yana goyon bayan duk 'yan kabilar Igho da su koma jijohinsu su kuma 'yan arewa su koma gida domin samun zaman lafiya.
Wani Alhaji Isa Saidu yace mutanen Igbo sun sha fada dole 'yan arewa su bar masu gari. Kabilar Igbo tana nunawa 'yan arewa wulakanci tare da yi masu barazana. Yace dare da rana suna cikin fargaba.
Ga rahoton Lamido Abubakar da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5