A Jihar Zamfara Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yansanda Uku

Babban sifeton 'yansandan Najeriya, Ibrahim K. Idris

Da alama yarjejeniyar da gwamnatin Zamfara ta cimma tare da 'yan bindiga dake satar mutane suna yiwa mutane kwace watannin baya ta rugurguje saboda yanzu 'yanbindigan sun koma bakin abun da suka saba yi inda suka sace yansanda uku a wani kauye jiya din nan.

Al'amuran kai hare hare da sace sacen shanu har ma da yin garkuwa da jama'a na cigaba da addabar jama'a a jihar Zamfara 'yan watanni bayan da gwamnatin jihar ta yi wani sulhu tsakanin Fulani 'yan bindiga da 'yan bangan yankunan.

Rahotanni sun ce jama'ar wasu kauyukan sun soma kaura daga gidajensu musamman a karamar hukumar Tsafe.

Lamarin baya bayan nan dai shi ne rahoton sace wasu jami'an 'yansanda uku daga garin Gyeda dake cikin karamar hukumar Tsafe da yammacin jiya inda kawo yanzu babu duriyar 'yansandan ko inda suke.

Wani ganao Haliru Magani yana mai cewa barayi ne suka je Kyeta suka dauke 'yansanda uku daga nan suka ratsa ta wani kauyen akan babura bakwai dukansu rike da bindigogi.

A cewar Haliru mutane na zaman dar dar koina saboda wannan ba shi ne karo na farko ba. Daga Gusau zuwa Magami an sha tare mutane ana kwace masu kudi da kaya.

Malam Haliru yayi mamakin yadda za'a ce gwamnati ta yi sulhu amma ta bar barayin da makamansu. Amma an bar mai laiffi da makami sai ya koma aikinsa,inji Haliru.

Rundunar 'yansandan jihar ta tabbatar da cewa an yi awan gaba da jami'anta uku a garin na Kyeta.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

A Jihar Zamfara Wasu 'Yan Bindiga Sun Sace 'Yansanda Uku - 2' 55"