An cafke Carl Ferer ne da wata takaradar iznin kama shi da hukumomin California suka bayar, bayan da ya isa birnin Houston da ke jihar ta Texas, yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa Amsterdam.
Babbar Attorney Janar din California, Kamala Harris, ta na zargin Ferrer da wasu abokanan huldarsa, da kafa shafin mata masu zaman kansu, wanda ya shahara a duniya, tare da baiwa masu aikata manyan laifukan damar tallata ayyukan ashsha a shafin.
A zahiri an yiwa shafin na Backpage.com rijista a matsayin shafin tallata ‘yan rakiya ga baki, amma kuma akan tallata kayayyaki da ayyuka a kansa.
Hukumar da ke karban haraji ta ce shafin na Backpage.com ya samu kusan Dala miliyan 51 a jihar ta California kadai a tsakanin watan Janairun shekarar 2013 zuwa watan Maris din shekarar 2015.