A jihar Taraba kungiyoyin lauyoyi da na kare hakkin dan Adam sun yunkura su tabbatar da an yi adalci biyo bayan harbin da ake zargin wani jami’in hukumar ta DSS a jihar da cewa ya yiwa wani magidanci da bindiga sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu akan hanyar mota.
Cin zarafi, da kisa da kuma wuce gona da iri na wasu jami’an tsaro na cikin matsalolin dake tada hankullan jama’a dama kungiyoyin kare hakkin bani adama a jihar Taraba, batun da masana ke kiran a yi bincike.
Na baya bayan nan shine harbi da bindiga da wani jami’in hukumar tsaro ta DSS, da aka bayyana sunansa da Husseini Dona dake aiki a gidan gwamnatin jihar Taraban, bisazargin cewa ya harbi wani mai sana’ar gyaran AC, Alhaji Audu Aminu Muhammad sakamakon takaddamar da ta hada su a hanyar mota.
Yanzu haka wanda aka harban, Alhaji Audu Aminu Muhammad na kwance a asibiti ana masa jinyar harbin bindigan.
Tuni wannan batu ya kai ga kungiyar lauyoyin jihar Taraban. Barrister Idris Abdullahi Jalo, shugaban kwamitin sa ido kan harkokin kare hakkin dan Adam, na kungiyar lauyoyin jihar ya tabbatar da faruwan lamarin da matakin da zasu dauka.
Shima wani dan rajin kare hakkin dan Adam a jihar Ahmad Gambo Daud, yace abun takaici ne wuce gona da irin da wasu jami’an tsaro ke yi a jihar, inda yace kusan wannan ne karo na biyar da ake samun irin wannan ta’asa na jami’an tsaro.
Yayin da kawo yanzu hukumar DSS a jihar ba tace komi ba, rundunan yan sandan jihar Taraba ta bakin kakakinta David Misal tace ta na bincike.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5