Wasu dinbin majiyanyata sun yi dafifi a Jalingo fadar jihar Taraban domin aikin duba lafiyar su kyauta da gwamnatin jihar ta gudanar da zummar tallafa wa marasa lafiya masu karamin karfi.
An dai gudanar da aikin ne a babban asibitin kwararru da ke Jalingo, hedikwatar jahar, inda aka yi wa wasu aiki na cututtukan da ke damunsu, yayin da wasu su ka samu magunguna.
Dr. Ranyang Akafa, wanda ya jagoranci aikin, ya ce sun shafe kimanin kwanaki uku suna wannan aikin kuma sun bai wa majinyata dubu daya da dari da hamsin (1,150) magunguna, sannan sun yiwa wasu majinyata sama da ashirin (20) aikin tiyata.
Dr Akafa, ya ce yanzu haka mata da kananan yara su suka fi yawa akan maza a wannan aiki na kwanaki uku.
Ga dai Ibrahim Abdul-Aziz da Cikakken rahoto:
Your browser doesn’t support HTML5