Jaririn da Bara'atu ta yankewa mazakutarshi kwanaki arba'in da uku da suka gabata ya shigo duniya.
Wannan mummunan lamarin wanda ya faru a kauyen Dape dake yankin karamar hukumar Shiroro yayi matukar tayar da hankulan mutanen dake zaune a yankin..
Muryar Amurka ta zanta da Bara'atu a hedkwatar 'yansandan jihar ta Neja. Akan ko ta san abun da ya kawota hedkwatar 'yansandan sai tace "na yi laifi" Tace ta yanka mutum. Da aka tambayeta ko menen ta yanke daga yaron sai tace "bura"
Bara'atu tace a gida ta yankewa jaririn zakarinsa . Bayan ta yake mazakutansa sai ta barshi nan wurin ta fita.
Yaron yanzu yana kwance a asibitin kwararru na IBB dake Minna. Dr. Ibrahim Abdullahi dake kula da yaron yace an yiwa yaron babban rauni saboda an yanke masa azzakarinsa gaba daya. Baicin hakan lokacin da aka kawo yaron da azzakrin ya riga ya mutu ba za'a iya sake dasashi ba kuma. Abun da ya rage yanzu shi ne hikimar kimiya kuma suna dubawa abun da za'a iya yi.
Mahaifin yaron, Muhammad Dauda wanda ya kidime yace watanni hudu ke nan da ya auri Bara'atu kuma bai santa da wani tabin hankali ba kuma bai taba samun wani sabani da ita ba.
Ma'aikatar kula da harkokin hakkin yara ta jihar ta dauki nauyin bin bahasin al'amarin kuma ta dauki nauyin maganin warkas da yaron. Barrister Maryam Kolo shugabar ma'aikatar tace hankalinsu ya tashi akan lamarin. Tace gwamnati zata dauki nauyin kula da yaron gaba daya.
Kakakin 'yansandan jihar DSP Bala Elkana yace da zara sun kammala bincike zasu gurfanar da matar gaban kotu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5