'Yan sakandaren Neja din suna rokon Allah ya kubutar da 'yan matan makarantar Chibok daga hannu 'yan kungiyar Boko Haram da suka sacesu kwanaki dari da suka gabata.
Hajiya Bilkisu Ndanusa darakta mai kula da makarantun sakandare a ma'aikatar ilimin jihar Neja ta bayyana dalilin shirya addu'o'in a daidai wannan lokacin. Tace 'yan matan da aka sace dalibai ne wadanda suke karkashin kulawar ma'aikatar ilimi dalili ke nan suka damu. Suna fatan Allah Ya sa a sako yaran ya kuma taba zukatan 'yan ta'adan.
Malam Dan Asabe Ibrahim Boso malamin makarantar sakandare yace irin wannan lamarin zai kawo cikas ga ilimi musamman a arewacin Najeriya. Idan ana sace dalibai daga makaranta yace gaskiya harkar ilimi zai samu koma baya a arewa. Yace suna neman alfarmar Ubangiji Ya sa a sako yaran.
Wasu daga cikin daliban sun ce sun ji abun da ya faru kuma suna fata Allah Ya sakosu lafiya. Gaskiya abun bashi da dadi kuma sun roki 'yan kungiyar ta Boko Haram su sako daliban domin a samu cigaba a harkar ilimi kuma hankalin iyayensu ya kwanta.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5