A Jihar Neja Wnda Ya Fitar da Diyarsa daga Makaranta Zai Fuskanci Hukunci

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

A kokarinta na tabbatar da cewa iyaye basu hana 'ya'yansu mata karatu ba gwamnatin jihar tace zata hukunta duk wanda ya fitar da diyarsa daga makaranta bisa ga sabuwar dokar da majalisar dokokin jihar tayi.

Gwamnatin tace ta dauki matakin ne domin tabbatar da cewa 'ya'ya mata sun sami ilimin da ya kamata.

Kwamishanan ilimin jihar Alhaji Danladi Abdulhamid yace akwai doka ta majalisa da ta tanadi hukunci. Duk wanda ya fitar da diyarsa daga makaranta zai biya nera dubu goma ko kuma yayi shekara daya a gidan kaso.

Majalisar dokokin jihar ta bayyana dalilin samar da dokar. 'Yar majalisa Sa'adatu Kolo shugabar kwamitin kula da harkokin mata da yara kanana a majalisar tace mutane na labewa da addini suna yiwa 'yarinya 'yar shekara goma ko goma sha biyu aure.

Daya daga cikin iyayen da aka zanta dasu yace ya yadda a bari yarinya ta gama ilimin sakandare kafin a yi mata aure domin a arewa akwai dalilan da zasu sa a bar yara mata su yi karatu. Yace a aikin kiwon lafiya mata na zuwa asibiti amma babu mata da zasu kula dasu.

Wata daliba dake aji uku yanzu a sakandare tace tafi son ta gama makaranta kafin a yi mata aure.

Yanzu dai gwamnatin jihar ta sanar cewa ranar 13 ga watan Oktoba za'a bude makarantun jihar domin samun damar yiwa malaman makarantu bita akan cutar ebola.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

A Jihar Neja Wanda Ya Fitar da Diyarsa daga Makaranta Zai Fuskanci Hukunci - 3' 06"