A Jihar California Wasu Masu Kishin Farar Fata Sun Farma Mutane

Wani dansanda na kokarin cafke daya daga cikin masu tada hankali

Jami'an tsaro na cigaba da binciken wani gangamin da 'yan tsananin kishin kasa Farar Fata su ka yi, wanda ya rikida zuwa tashin hankali ranar Lahadi a birnin Sacramento da ke yammacin kasar a jihar California, wanda ya yi sanadin jikata mutane 10, biyu daga cikinsu da tsanani.

Mai magana da yawun hukumar kare hadura George Granada ya gaya ma Muryar Amurka cewa za a gudanar da bincike mai zurfi, yayin da 'yansanda ke neman bayanai daga shaidun ganin ido, da bidiyo da kuma al'umma.

Gangamin a wajen Majalisar Dokokin jihar California da wata kungiya ta mutane 30 ce ta shirya. Kungiyar Farar fata tsantsa ta 'yan kishin kasa, wacce ake kira Traditionlist Workers Party, ta fito ne bayan da wasu masu zanga-zanga da suke adawa da kungiyar su wajen 400 suka fara fitowa sai fada ya kaure.

Jami'an sun ce an yi jinyar wadanda aka sokesu ko su ka kuje ko kuma aka daba masu wuka. Faya-fayen bidiyon da aka saka a yanar gizo na nuna yadda ake ta kai naushi ma mutane da dama tare da bugunsu da kafa har da sanduna.