An dai bude ofishin hukumar EFCC na jihar Borno a ranar 22 ga watan Maris na shekara ta 2011, wanda aka rufe ofishin sakamakon dalilan tsaro aka kuma sake budewa a watan Nuwambar 2015. Cikin wannan lokacin ne ofishin hukumar EFCC ya gano kudaden.
A wata sanarwa da shugaban hukumar na jihar Borno Ibrahim Baffa, ya aikawa manema labarai, sai dai sanarwar bata bayyana irin mutanen da aka karbo kudaden daga hannunsu ba, ko kuma hukumomin da suka mayar da irin wadannan kudade. Amma kuma cikin makonnin nan ne dai aka dinga ganin gwamnatin jihar Borno na musanyawa wasu jami’an gwamnatin guraren ayyuka. Wadanda kuma ake zarga da cin kudaden daruruwan ma’aikata na buge, wanda aka gano sune sakamakon ci gaba da tantance ma’aikata da gwamnatin jihar Borno ke yi.
Hukumar EFCC sun gurfanar da wasu manyan jami’an Asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri a gaban wasu kotuna, wanda ake zarga da yin sama da fadi da wasu kudaden asibitin. EFCC dai na ci gaba da yin dirar mikiya kan hukumomi da ma’aikatun gwamnati a jihar Borno, sakamakon yawan korafe korafen da ake samu.
Sanarwar da hukumar ta fitar dai na cewa ya kamata ‘yan kasuwa da suka hada da mata da maza su dinga mayar da hankali wajen kasuwancinsu don gudun kar a jefa su cikin wani hali a cewar hukumar, kuma a shirye take ta sa kafar wando guda da duk wanda ta kama.
Daga karshe hukumar tayi kira ga jama’a da su ringa kai rahotannin duk wanda suke zargi da cinye dukiyar jama’a zuwa ofishin shugaban hukumar don daukar matakin da ya kamata akan duk wanda ake zargin.
Your browser doesn’t support HTML5