Alhaji Ado Daukaka wani mawakin siyasa ne kuma tun ranar Jumma’ar da ta gabata da ya fita har yanzu ba’a ganshi ba.
Wannan lamarin ya kara jefa iyalansa da masoyansa cikin wani mawuyacin hali. Haka ma hukumomin tsaro a jihar Adamawa sun tabbatar da bacewar mawakin wanda ya bace jim kadan bayan ya fitar da wata waka mai taken “Gyara Kayan Ka”.
Wannan sabuwar wakar tayi allawadai ne da halayen wasu ‘yansiyasar jihar.
Iyalansa da ‘yanuwansa sun shaidawa Muryar Amurka cewa sun yi masa ganin karshe ne a ranar Juma’a kuma har yanzu basu san idan yake ba. Daya daga cikin matansa Malama Hadiza Dauda wadda ta haihu kwana kwanan nan tace ya fita da zummar zuwa shagonsa ne kuma tun daga lokacin bai koma gida ba.
Matansa sun yi kokarin kirar lambar yawarsa amma bata tafiya. Sun yi cigiya da sanarwa amma har yanzu shiru babu labari. Suka ce su basu san abun da ya yi ba amma suna roko da sunan Allah a taimaka a sakoshi.
Kamar iyalansa ita ma da take nuna damuwarta, hadakar kungiyar mawakan jihar ta yi tur da abun da ya faru tare da kiran wadanda suka saceshi su yiwa Allah su sakoshi sakamakon alfarmar wannan watan Ramadan.
Malam Hassan Ahmed Albadawi da ake yiwa lakabi da “Ko Ka Ga Budurwa”, shugaban kungiyar mawakan Adamawa ya bayyana halin da ake ciki a yanzu. Yace suna rokon wadanda suka saceshi su dubi girman wannan watan su sakoshi ya dawo cikin iyalansa.
Rundunar ‘yansandan jihar ta baza jami’anta domin neman mawakin. ASP Usman Abubakar kakakin rundunar ‘yanasandan ya bayyana irin kokarin da suke yi a yanzu.
Tuni dai mutane suka soma ta'allaka bacewar mawakin da sabuwar wakar da ya yi wadda ta soki lamirin ‘yan siyasar jihar.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5