A Janhuriyar Nijar, Kwamitin Kyautata Hulda da dangantaka tsakanin mabiya addinai, wanda ke karkashin ofishin Ministan Cikin Gida, ya sa harkokin mabiya addinin Musulunci da na Kirista cikin harkokinsa saboda su yi harkokinsu kafada da kafada da juna. Ta yadda mabiya addinan za su rinka shaida ma Kwamitin duk wata harkar da za ta gudanar.
Da ya ke bayani ga manema labarai, Babban Sakataren Kwamitin Malam Abdulsamadu Yahaya ya ce musabbabin wannan matakin shi ne a zauna lafiya tsakanin bangarorin. Malam Yahaya ya jaddada cewa daga kungiyoyin na addini za su rinka gudanar da harkokinsu ne da sanin Kwamitin. Ya ce bangarorin addinan za su rinka ba da shawara ga Kwamitin duk kuwa da cewa Kwamitin zai rinka sa ido kan abubuwan da kungiyoyin addinan ke aiwatarwa, don a yi aiki tare wajen tabbatar da zaman lafiya; da kuma kokarin kawo karshen bara a kasar.
Wanda ya turo ma na da wannan rahoton, wakilnmu a Janhuriyar Nijar Shu’aibu Mani ya ruwaito Malamin addinin Musulunci mai suna Umar Tasi’u ya na cewa abin farin ciki ne samun masu ba da shawara kan gudanar da duk wata haraka ta addinin Musulunci. Shi ma Fastor Hashimu Yahaya ya ce abin da Kwamitin ya fada ya gamshe su.
Your browser doesn’t support HTML5