A Jamus 'Yansanda Sun Kai Samame Hedkwatar FIFA

Ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus

Yan sanda a Jamani sun kai samame a hedikwatar hukumar kwallon kafa ta kasar da kuma gidajen mutane ukku wadanda suke manya-manya ne a cikin hukumar.

Wannan ko ba zai rasa nasaba ba da bikin daukar dawainiyar nauyin wasan kwallon kafa na duniya da akayi a cikin shekarar 2006.

Babban mai gabatar da kara na kasar Nadja Niesan yace kai wannan samamen sakamakon tuhumar da ake yi na kaucewa biyan haraji a wannan lokacin wanda hakan kuma babban laifi ne, musammam ma da yake ya shafi hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

A labarin da wata mujalla mai suna Der Spiegel ta buga a cikin watan da ya gabata, tace ana tuhumar cewa hukumar ta kwallon kafa ta Jamanin ta baiwa jamiaan na FIFA toshiyar baki har na dala miliyan 7.4 domin samun kuri’u masu rinjaye na samun damar daukar dawainiyar gudanar da wasan a shekarar ta 2006.

Kasar ta Jamani dai ta buge abokiyar karawar ta ce wato Africa ta Kudu da kuria guda lokacin da aka zo neman wannan damar