An cafke mutane biyar – ciki har da dan wata kasar Afrika ta Yamma – a kasar Jamus a bisa zargin cewa suna son su zama ‘yan jihadin kungiyar IS.
WASHINGTON DC —
Ministan shara’a na Jamus din, Heiko Mass yace kama wadanan mutanen ba karamin ci baya ne ba ga ita kungiyar ta IS.
Hukumomin Jamusawan sunce an cafke wadanan mutanen ne a lokacin wani samamen da aka kai a yankunan Saxony da Rhine Westaphalia, kuma an kama su yayinda suke kokarin samarwa IS mutanen da zasu je suyi mata yakin jihadi a kasar Syria.
Daya daga cikin wadanda aka kaman wani Balaraben kasar Iraq ne mai lakabin Abu Wala, 32, wanda aka ce shine madugun rukunin mutanen.
Sauran sun hada da dan kasar Turkiya, da dan kasar Jamus, da dan kasar Serbia da kuma dan kasar Kamaru.