A Iraqi Yakin Fallujah Na Kara Rutsawa da Farar Hula

Dakarun Iraqi da suka kewaye birnin Fallujah

Dakarun Iraqi da suka kewaye birnin Fallujah

Rahotanni daga Iraqi suna nuni da cewa yawan fararen hula wadanda yakin kwato birnin Fallujah ke rutsawa da su yana karuwa sosai, wannan ya biyo bayan matakin da dakarun gwamnatrinn kasar da wata kungiyar mayakan sakai ta 'yan shi'a da take marawa gwamnati baya suke yi

Kamar yadda aka ji daga bakin wani babban jami'in majalisar kula da 'yan gudun hijira daga kasar Norway take cewa halin da farar hula ke ciki nada ban tausayi

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ta sami rahotannin cewa ana kashe farar hula sakamakon amfani da manyan makamai, wasu kuma baraguzan gine ginen gidajensu da suka fadi sun danne su.

"Haka nan akwai rahotannin cewa daruruwan iyalai ne aka ce kungiyar ISIS take amfani da su a zaman garkuwa" na hana akai musu hari, inji kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD William Spindler.

Ahalinda ake ciki kuma a Syria, jiragen yaki da ake kyautata zaton na kasar Rasha ne, sun yi luguden wuta kan birnin Idlib dake hanun 'yan tawaye, suka kashe akalla mutane 50 suka jikkata wasu masu yawa, sannan da wasu da ake jin gine-gine da suka rushe sun danne su.

Mutanen Fallujah da suka samu tserewa daga birnin

Mutanen Fallujah da suka samu tserewa daga birnin