A Hukumance Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Ayyukan Kungiyar Shi’a

Mai Magana Da Yawun Gwamnan Jihar Kaduna Samuel Aruwan

Gwamnatin jihar Kaduna tace rashin amincewa da hukumomi da kuma dokokin ‘kasa ne yasa ta haramta dukkan harkokin kungiyar Shi’a da ake kira IMF a jihar.

Da yake jawabi gaban manema labaru mai magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, yace gwamnatin jihar ba tana nufin haramtawa mutanen jihar yin addinansu bane, sai dai abubuwan da kungiyar Shi’a ke yi sun sabawa doka. Hakan yasa gwamnatin jihar tayi amfani da hujjojin da kwamitin majalisar zartarwa ta fitar wajen daukar matakin haramta ayyukan kungiyar, wadda kuma ta fara aiki tun ranar da aka aiwatar.

Sai dai kuma sakataren yada labaru na kungiyar Shi’a Mallam Abdulmuminu Giwa ya musanta dukkan zargin da ake yiwa kungiyar. Da yake mayar da martani kan cewa akwai abubuwan da kungiyar ke yi da suka sabawa dokar kasa, Mallam Abdulmuminu yace “bamu yarda da kasa ba, ba sai su fadi cewa ga inda muka yanke mukace shine namu kasar ba, fasfo din Najeriya muke amfani da shi, muna kashe Naira, duk inda muka fito sunanmu ‘yan Najeriya sannan kuma ace bamu yarda da dokar kasa ba.”

Kasancewar gwamnati tazo matakin karshe inda ta fitar da dokar da ta haramta ire iren tarurrukan mabiya mazahabar Shi’a, Mallam Abdulmuminu yace wannan magana ce ta doka kuma akwai kotu, kuma shugabannin kungiyar zasu duba suga matakan da suka dace.

Saurari cikakken rahotan Isah Lawal Ikara.

Your browser doesn’t support HTML5

A Hukumance Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Haramta Ayyukan Kungiyar Shi’a - 3'47"