Tsohon ‘dan wasan Najeriya Henry Nwosu, ya gargadi hadaddiyar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, kan kada ta roki ‘yan wasan da suke ‘yan Najeriya da su bugawa kungiyar Super Eagles wasa.
A kwanannan ne dai shugaban hadaddiyar kungiyar kwallon kafa Amaju Pinnick, ya ziyarci iyayen Chuba Akpom da Alex Iwobi a can Ingila, domin rokarsu dasu bar ‘ya ‘yan su bugawa kasarsu wasa.
Haka zalika Najeriya na bin diddigin ‘dan wasan nan Jordan Ibe dake bugawa kungiyar Liverpool wasa, amma Henry na ganin Jordan Ibe bai fi Kelechi Iheancho ko sauran ‘yan wasa irin na Flying Eagles da Golden Eaglets iya wasa ba.
A wata hira da gidan jaridar Punch tayi da Henry Nwosu, yace idan Jordan Ibe da sauran ‘yan wasan Najeriya basa son bugawa kasar su wasa, to Allah ya taimakesu. Ba zasu zamanto ‘yan wasa na farko ba da suka ki bugawa Najeriya ba. ya cigaba da cewa, daga karshe sune zasuyi dana sani, idan muka neme su dasu bugawa Super Eagles wasa suka ki, sai kawai mu kyale su.