A Brazil Kotun Koli Ta Takawa Nadin Lula A Zaman Minista Birki.

Masu zanga zanga a Brazil, suna kiran d a a tsige shugabar kasar Dilma Rousseff, da kuma batun nada ubandakinta tsohon shugaba Lula Inacio da Silva.

Kotun kolin tace nada Lula da Silva tamkar cin fuska ne ga tsarin mulkin kasar.

A Brazil, wani alkalin kotun kolin kasar ya hana tsoshon shugaban kasar Luiz Inacio da Silva, karbar mukami a majalisar ministocin kasar, mataki da zai bashi kariya daga fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa a binciken da ake yi akansa haalin yanzu.

Alkali Gilmar Mendes, wanda ya fidda hukuncin da ya yanke a daren jiya jumma'a, yace baiwa tsohon shugaban kasar mukami a majalisar ministoci zai "kasance " hawan kawara ne ko rena tsarin mulki."

A Brazil ministocin kasar suna da kariya daga shari'a a gaban kotunan kasar kan zargi aikata laifi, amma ana iya gurfanar da su gaban kotun koli.

Shirin shugabar kasar Dilma Rousseff na nada tsohon shugaban kasa Lula, a majalisar ministocin kasar wanda ya janyo cece-cece kuce, da zai iya baiwa tsohon shugaban kasar kariya daga fuskatar tuhuma cin hanci da rashawa da kuma halatta kudaden haram.

Masu bincike suna zargin hakan ya auku ne a ma'aikatar man kasar.