Wani rahoto mai kakkausar lafazi da kwamitin Majalisar dokokin Birtaniya ya fitar a jiya Talata, ya nuna cewa, har yanzu mutanen da ke cin zarafin mata ta hanyar lalata da su, na ci gaba da samun ayyukan yi a kungoyiyon agaji na kasa da kasa, inda sukan yi amfani da wannan damar su rika lalata da yara kanana da ‘yan mata da kuma mata.
Kwamitin har ila yau, ya zargi fannin kungiyoyin agaji da hadin kai wajen marawa wannan aika-aika baya.
‘Yan majalisa a karamar majalisar dokokin Birtaniya da ke kwamitin raya kasa da kasa, sun ce, watanni bayan da aka fallasa ayyukan lalata da ma’aikatan agajin Birtaniya suka yi a Haiti a karon farko, har yanzu bangaren kungiyoyin da ke ayyukan agaji na kasa da kasa, ba sa tabuka wani abin a zo-a-gani, wajen aiwatar da matakan yakar maza masu irin wannan mummunar dabi’a.