Kwamishinan cibiyar kare hakkin bil adama ta MDD din, Zeid Ra’ad ya yi kira ga hukumomi a Philippines da su kaddamar da gagarumin bincike a kan maganar kisa da shugaba Duterte ya yi a ranar Juma’a inda yace ya harbe kuma ya kashe akalla mutane uku a lokacin da yake rike da mukamin magajin garin Davao.
Zeid yace wani abin al’ajabi ne ace akwai wani tsarin shara’a da ba zai himmatu wajen gudanarda bincike da kuma shirya daukan matakan shara’a akan duk wani da ya fito, da bakinsa, yace ya kashe wani ko wasu ba.
Duterte ya fada a cikin jawabansa a kwana kwanannan cewa a can baya, lokacin yana magajin garin na Davao, ya sha zagaya garin akan babur yana neman bata-gari, yana kuma kashesu don yan sanda su yi koyi da shi.