A Bari Ya Huce: Labarin Wakilin Boge, Octoba, 26, 2019

Alheri Grace Abdu

Mun kawo maku labarai uku a shirin A Bari Ya Huce na wannan makon da suka hada da labarin maigida da magen amaryarsa da kuma wakilin boge.

MAGE MAI SANIN GARI

Wani mutum ne matarsa ke da mage, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta, ya yi tafiya mai nisa da ita cikin daji da motarsa. Ya aje motar, ya dauki magen ya yi tafiya mai nisa da ita cikin dajin nan, ya jefar da ita. Ya kama hanyar dawowa sai ya yi makuwa, ya rasa inda ya aje motar. Ya wuni yana garari cikin jeji ya kasa sanin inda ya ajiye motarsa. Bayan yaci yawo ya gaji, can da la'asar yaga babu sarki Sai Allah ba kuma alamar wani mahaluki a jejin da zai nuna mashi hanya. sai ya buga wa matarsa waya, ya gaya mata abinda ya yi da kuma halin da yake ciki. Bude bakin matar ke da wuya sai ta ce: “Ai kuwa bayan tafiyarka da sa'oi biyu magen ta shigo gida. ban san tare kuka fita ba” Shi kuwa sai ya kara rudewa, ya ce wa matar: “Ba magen waya mu yi magana da ita”

WAKILIN BOGE

Wani dan siyasa ya je wani kauye; ya tambaye su matsalolisu. Suka ce manyan matsalolinmu biyu ne! Ta farko: Muna da asibiti amma ba likitoci. Nan take sai dan siyasar ya fito da wayarsa yana buga waya na karya, da ya gama magana da iska. shi kadai, sai ya dubi jama'a yace da su mun gama shiri, gobe za a turo maku likita. Mecece kuma matsalarku ta biyu? Suka ce matsalarmu ta biyu; babu network a garinmu baki daya. Wannan ya nuna wayar da yake yi ta boge ce kawai. Ashe bai sani ba babu hanyar waya a garin.

Your browser doesn’t support HTML5

A Bari Ya Huce- Labarin Wakilin Boge-23:00"