A BARI YA HUCE: Labarin Dan Fulani Da Barayi- Agusta, 29,2020

Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun bada labarin wani bafulatani da ya shiga mota zai je tafiya, sai 'yan fashi suka tare su,da ya ga haka ya fito mota ya zura a guje cikin jeji

Bayan barayi sun gama binciken mutanen da ke cikin mota sai suka ce "ina da ke zaune nan?" Sai fasinja suka ce dan fulani ne kuma ya gudu. Sai shugaban barayin ya ce in dai dan fulanin asali ne zai zo hannu, ya umarci barayin su shiga jeji su kira sau uku zai fito.

Barayin suka shiga jeji suna kiran Bafullatani, bayan sun kira shi sau uku bai amsa ba, sai kuma koma suka cewa shugabansu wanda yake zaune karkashin wata bishiya cewa, su hakura kawai Fulani ya tsare, ashe dan fulani na saman bishiya yana kallon su, sai gogan naku ya ce "ba sau uku kuka kira ni ba Aradun Allah ko sau dubu za ku kira ni ba zan fito ba.

Saurari cikakken shirin ka sha dariya.

Your browser doesn’t support HTML5

A BARI YA HUCE: Labarin Dan Fulani Da Barayi -28:00"