A zaman taron da rundunar sojin ta shirya a Yola tsakanin al'ummomin da suka koma yankuanansu an samu labarin cewa wasu na nunawa junansu yatsa tare da zarginsu da kawo kungiyar Boko Haram.
Wani shugaban al'umma a wurin taron ya kira sojoji da su taimakesu kawo zaman lafiya tsakaninsu musamman a yankunan Madagali da Michika da Mubi ta arewa da kudu. Cewa musulmi ne suka kawo Boko Haram ba zai taimaki zaman lafiya ba kamaar yadda suke da.
Janar Rogers Nicholas babban hafsan soji dake kawo fahimtar juna tsakanin fararen hula da kuma soji yace ba za'a anye sojoji yanzu ba. Ya kuma yi gargadin cewa ba zasu kyale duk wani da aka kama yana daukar doka a hannnusa ba ko kuma wanda yake neman kawo baraka a cikin al'ummomin dake komawa..
Yace aikin soji ne su kare 'yan kasa da kuma kasa. Saboda haka sojoji ba zasu tashi daga yankin yanzu ba. Duk wanda aka kama yana rura wutar gaba ko gyama ba zai ji da dadi ba. 'Yan ta'ada babu ruwansu da addini ko kabila. Yace duk wanda ya dauki doka a hannunsa to ya kuka da kansa.
Amma al'ummomin yankin suna kokawa da karancin jami'an tsaro da ababen more rayuwa lamarin dake tsorata wasu da komawa yankinsu..
Wani daga Michika yace suna cikin kuncin rayuwa. Jin dadin rayuwa shi ne tsaro na biyu kuma yara su samu makaranta da kuma na uku kiwon lafiya. Yace kawo yanzu basu da jami'in kiwon lfiya ko daya. Babu kuma jami'an tsaro.
Kungiyoyin sa kai sun bukaci a samu fahimtar juna da shirya bitoci na watanni takwas. Zasu yi fadakarwa a gidajen radiyo da jaridu.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5