Shugabar shirin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya Malama Lantana Abdullahi tace an tsara shirin don fadakar da ‘yan jarida muhimmancin anfani da rahotanni da suke wallafawa ta auna bayanai da suke tattarawa da tantance labarun da suke wallafawa ta kafofin yada labarai ta yadda ba zasu kara ruruta wutar rashin fahimtar juna ba, ko hana zaman lafiya da harzuka jama’a waje tuna masu abinda ya abku a baya maimakon dinke banbance banbancensu.
Wasu ‘yan jarida Yakubu Uba da George Kushi da Murya Amurka ta yi hira da su, sun bayyana bitar da cewa sara ce kan gaba, ganin kokarin da jihar Adamawa da a baya ta yi fama da rikicin ta’addanci ke neman mafita daga radadin da suka yi fama da ita ta hanyar kyautata fahimtar juna da samar da dawamammiyar zaman lafiya.
Bayaga samarwa ‘yanjaridan damar sanin makamar aiki, Kungiyar Search For Common Ground ta kafa jidauniyya ga masu niyyar gudanar da bincike mai zurfi kan lamuran da ke ci wa jama’a tuwo a kwaryada tallafin kudi.
Ana saran ‘yanjaridan zasu koyi sabbin dabarun tattara bayanai da sarrafasu ta yadda zasu taimaka wajen sasantawa, kara fahimtar juna da samar da dawamammiyar zaman lafiya a bayan kammala bitar wadda zata dauki tsawon yini biyar.
Ga rahotn Sanusi Adamu da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5